Hukumar
EFCC ta musanta zargin da PDP ta yi cewa ta kai samame a gidan 'ya'yan
dan takararta na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.
A wasu jerin
sakwanni da ta wallafa a Twitter, EFCC ta ce ta kai kai farmaki ne a
gidan 'ya'yan tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji a Maitama wanda
take gudanar da bincike a kansa.Kuma 'ya'yan tsohon gwamnan na Abia suna makwabtaka ne da Aliyu da Mustapha Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019.
Sai dai kuma Jam'iyyar PDP ta yi zargi cewa, EFCC ta kai samamen ne a gidan 'ya'yan na Atiku bisa umurnin fadar shugaban kasa.
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin, inda mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya soki PDP da yada labaran karya.
"A Najeriya yanzu babu wanda ya fi yada labaran karya kamar jam'iyyar PDP," in ji Garba shehu a sakon da ya wallafa a Twitter.
- Amurka da EU na son a rungumi kaddara 'kan Buhari da Atiku'
- Jami’an tsaron Najeriya 'sun binciki Atiku'
Hukumar ta ce ta kai ga kama 'ya'yan tsohon gwamnan ne ta hanyar bin sawun wasu manyan motocin da aka ce nasu ne.
Kuma a lokacin da take tatasar bayanai ne suka bayyana mata gidan da suke zama a Abuja da ta kai samame a ranar Asabar.
EFCC ta ce bincikenta da ta gudanar bai shafi gidan 'ya'yan Atiku ba.
Sai dai a cikin bayanan da ta wallafa a Twitter, hukumar ba ta ce ko ta leka sashen gidan 'ya'yan Atiku ba da suke gida guda da 'ya'yan tsohon gwamnan na Abia da ta kama.
CULLED FROM @BBCHAUSA


Comments
Post a Comment