Shugabannin kasashen Kungiyar
bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS sun
gudanar da wani taron yini daya a Abuja.
Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron wanda shi ne na 54 inda aka
tattauna batutuwan da suka shafi yankin na yammacin Afirka.Wasu batutuwa da taron ya mayar da hankali a kai sun hada da batun samar da kudin bai-daya tsakanin kasashen yankin.
Taron ya mayar da hankali kuma kan yaki da ta'addanci da rikicin siyasa a kasashen Togo da Guinea Bissau.
- Najeriya: Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 na N8.83tr
- APC 'ta jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa'
- Sojin sama na Nijar na mutuwa a wajen horo
Shugabannin kasashen na ECOWAS sun dauki mataki game da rikicin na Togo musamman bayan kammala zabe a ranar Alhamis.
Sun amince a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar.
Taron dai na zuwa mako daya bayan taron da aka gudanar a Abuja na shugabannin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.
A wajen taron Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Chadi Idris Deby da Mahamadou Issoufou na Nijar da kuma Paul Biya na Kamaru sun amince da tsarin wasu bukatu guda takwas domin kawo karshen yaki da kungiyar Boko Haram da ta addababi yankin
Culled from BBCHAUSA

Comments
Post a Comment