Dan takarar
jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya sanya hannu a kan takardar
yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zabukan da za gudanar a shekara mai
zuwa.
Shugaban jam'iyyar ta PDP Uche Secondus ne ya bayyana haka a shafinsa na Tiwita.Mista Secondus ya bayyana cewa ya jagoranci Atiku Abubakar zuwa cibiyar Bishop Kukah da ke Abuja inda ya sanya hannu a kan yarjejeniyar.
- Atiku Abubakar ya kaurace wa taron zaman lafiya
- Dalilin da ya sa Atiku ya kauracewa taron zaman lafiya
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Amma Atiku Abubkar bai halarci taron ba duk da cewa tsohon shugaban Najeriya Abdussalam Abubakar wanda shi ne ke jagorantar wannan kokarin ya ce kwamitinsa ya gayyaci dukkan jam'iyyun siyasar kasar zuwa wajen wannan taron.
Culled from @bbchausa

Comments
Post a Comment