CSKA ta ragargaji Real Madrid a Bernabeu

CSKA Moscow ta ragargaji Real Madrid a Spaniya da ci 3-0 a wasan karshe na cikin rukuni a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League.
Wannan ne karon farko da aka ci Madrid kwallaye da dama a gida tun bayan shekara tara a gasar ta Zakarun Turai.
Real wadda ke rike da kofin bara, tuni ta kai zagayen gaba a wasannin bana a rukuni na bakwai, ana ganin hakan ne ya sa ba ta fara karawar da manyan 'yan kwallonta ba.
Bayan kammala wasan magoya bayan Real Madrid sun yi wa 'yan wasansu ihu a Santiago Bernabeu.
CSKA Moscow, wadda wasa biyu kacal ta ci a rukuni har da wanda ta doke Madrid ta fice daga wasannin shekarar nan, bayan da Viktoria Plzen ta ci Roma 2-1 ta kuma samu gurbin shiga gasar Europa League.

Culled from BBCHAUSA

Comments