Wata babbar kotun jihar Kano a
Najeriya ta haramta wa majalisar dokokin jihar gudanar da bincike a kan
wani hoton bidiyo da ke nuna Gwamna Abdullahi Ganduje yana karbar wasu
daloli da ake zargin cin hanci ne.
Wata kungiyar lauyoyi masu
fafutukar kare demokuradiyya ne suka shigar da karar, inda suka
kalubalanci majalisar cewa ba ta da hurumin gudanar da binciken. Kotun wadda mai shari'a Ahmad Tijjani Badamasi ya jagoranci zaman nata ta amince da bukatun da bangaren mai karar ya gabatar mata, ciki har da haramta wa majalisar gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje, kasancewar yana da rigar kariya, kuma ba aikin majalisar ba ne gudanar da bincike a kan miyagun laifuka.
- Ganduje ya yi magana kan bidiyon zargin karbar rashawa
- Sheikh Ibrahim Khalil: Na raba gari da Gwamna Ganduje
- Hotunan yadda zaman majalisar Kano da wakilin Ganduje ya kasance
Barrister Mohammed Zubairu shi ne shugaban kungiyar lauyoyi masu rajin kare demokuradiyya a Najeriya, wanda ya shigar da karar a madadin kungiyar, kuma ya ce wannan nasara ba ta su ba ce ta demukradiya ce.
Shi kuwa Barrister Mohammed Waziri lauyan da ya tsaya wa majalisar dokokin jihar Kano, cewa ya yi za su kai al'amarin ga majalisa domin yin nazari kan mataki na gaba, na daukaka kara ko a'a.
Wannan hukuncin dai za a iya cewa babban cikas ne ga yunkurin majalisar dokokin na ikirarin da ta yi cewa za ta bi diddigi har sai ta gano gaskiyar lamarin.
Wani, danjarida, Ja'afar Ja'afar ne dai ya fara wallafa hotunan bidiyon a jaridarsa ta intanet, lamarin da ya ja hankalin majalisar dokokin jihar Kano ta fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa gwamnan.
Bayan wannan kotun ma, akwai wata shari'ar a gaban wata babbar kotun jihar Kanon, inda Gwamna Ganduje ya shigar da karar dan jarida Ja'afar Ja'afar, yana zarginsa da yi masa kazafi, kana ya nemi kotu hana shi ci gaba da yada hotunan bidiyon, tare da biyan gwamnan diyyar naira miliyon dubu uku ta bata masa suna.
Culled from @BBCHAUSA

Comments
Post a Comment