Theresa May: 'Yan majalisa za su kada kuri'a kan Brexit

Firai ministar Birtaniya Theresa May za ta fuskanci kuri'ar amincewa da shugabancinta da yammacin ranar Laraba.
A lokacin da ta ke jawabi a gaban ofishin firai minista da ke gida mai lamba 10 a Downing Street, ta ce: "Zan nemi amincewar dukkan 'yan majalisa dangane da wannan kuri'ar da za a kada."
Ta kuma ce idan ta fadi, dole ne sabon firai ministan da aka zaba ya soke dokar Article 50 ta ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, wadda aka tsara yi ranar 29 ga watan Maris.
"Wannan na iya dakatar da shirin ficewar Birtaniya daga Turai gaba daya," inji ta.
'Yan majalisa daga jam'iyyarta ta Conservative za su fara kada kuri'a a kan batun daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 8 na dare agogon GMT.
Ana sa ran a fitar da sakamako bayan sa'a guda.
Wannan kokarin na tsige Misis May ya biyo bayan wasu wasiku 48 da 'yan majalisa suka mika na neman a sauya shugabancin jam'iyyar kamar yadda tsarin majalisa ya tanada.

Culled from bbchausa

Comments