Amina Zakari: Ba ni da dangantaka da Buhari

Kwamishinar ta hukumar zaben Nijeriya INEC Amina Zakari ta musanta cewa tana da dangantaka ta jini da shugaba kasar Muhammadu Buhari.
Wasu 'yan siyasar kasan ne dai suka fara zarge-zargen cewa tana da dangantaka da Buhari, don haka suna da shakku kan adalcin da INEC za ta yi a zaben dake tafe.
An nada Amina a matsayin mai kula da tattara sakamako, abinda ya sa 'yan adawar ke ganin za a yi musu magudi.
Ko a shafinsa na twitter, mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar Garba Shehu ya ce jami'ar ba ta hada dangantaka ta jini da shugaban ba, illa iyaka dai akwai wata alakar auratayya tsakaninta da wasu daga cikin dangin shugaban kasar.
Sai dai ko a daya daga cikin shirye-shiryenmu, mun kawo ma ku wata hira da Shehu Yusuf Kura na jam'iyyar PDP inda ya bayyana irin wannan korafi game da nadin na Hajiya Amina Zakari.

Culled from BBCHAUSA

Comments