
Tsohon
mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar
PDP, Atiku Abubakar, ya isa kasar Amurka a yammacin ranar Alhamis.
Kamar
yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, ya je kasar ne domin tattaunawa
da jami'an kasar da kuma 'yan Najeriya mazauna kasar.
- Zan sayar da NNPC ko za a kashe ni —Atiku
- Da gaske EFCC na farautar 'ya'yan Atiku?
- Atiku ya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
"Yanzunan
na sauka a birnin Washington D.C domin ganawa da jami'an gwamnati da
kuma 'yan Najeriya mazauna kasar da kuma yan kasuwa."
Tsohon
mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar shugaban majalisar dattawan
Najeriya Bukola Saraki, wanda shi ne Darakta Janar na kamfe dinsa.
Wasu
na zargin tsohon mataimakin shugaban kasar ne da kasa zuwa Amurka
saboda zargin da aka ce kasar na yi masa na cin hanci da rashawa.
Zargin da ya sha musantawa a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.
CULLED FROM BBCHAUSA
Comments
Post a Comment