Real Madrid za ta ziyarci Leganes, domin fafatawa a wasa na biyu a Copa del Rey a yammacin Laraba.
Tuni kocin Real, Santiago Solari ya bayyana 'yan wasa 19 da za su buga karawa da Leganes a wasan kungiyoyi 16 da suka rage a Copa Del Rey.
Madrid ta yi nasarar cin wasan farko da ci 3-0 a Santiago Bernabeu da suka fafata a ranar 9 ga watan Janairu.
Ga 'yan wasan da za Madrid ta je da su Butarque.
Masu tsaron raga: Keylor Navas da Luca da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da Reguilón da kuma Javi Sánchez.
Masu buga tsakiya: Casemiro da Valverde da Isco da Ceballos da Brahim da kuma Jaume.
Masu cin kwallaye: Lucas Vazquez da Vinicius Jr. Da kuma Cristo.
CULLED FROM BBCHAUSA

Comments
Post a Comment